Mark 11

1Da suka kusa Urushalima, kusa da Betafaji, da Betanya, wajen dutsen zaitun, sai Yesu ya aiki almajiransa biyu 2ya ce masu, “ku shiga kauyen can kusa da mu. Da zarar kun shiga za ku ga aholaki a daure, wanda ba a taba hawa ba. Ku kwance shi, ku kawo mani. 3In wani ya ce maku, “Don me kuke haka? ku ce, ‘Ubangiji ne yake bukatarsa, zai kuma komo da shi nan da nan.”’

4Sai suka tafi, suka tadda aholakin a daure a kofar gida a bakin hanya, suka kwance shi. 5sai wadanda suke tsaye a gun suka ce masu, “Don me kuke kwance aholakin nan? 6Suka fada masu abinda Yesu yace, sai suka kyale su suka tafi.

7Almajiran nan biyu suka kawo wa Yesu aholakin, suka shimfida mayafansu a kai, sai ya hau. 8Sai mutane da yawa suka shimfida mayafansu a hanya, wadansu kuma suka baza ganyen da suka yanko daga filayen. 9Wadanda suke gaba da shi da wadanda ke bin bayansa suka yi sowa suna cewa, “Hosanna! Albarka ta tabbata ga mai zuwa cikin sunan Ubangiji. 10Albarka ta tabbata ga mulkin nan mai zuwa na Ubanmu Dawuda! Dukaka a cikin sama!”

11San nan Yesu ya shiga Urushalima, ya shiga Haikalin. Sai ya dudduba komai, da magariba ta yi, ya fita ya tafi Betanya tare da goma sha biyu nan. 12Kashe gari, suka tashi daga Betanya, sai ya ji yunwa.

13Da ya hango itacen baure mai ganye daga nesa sai ya je ya ga ko za sami ‘ya’ya. Da ya iso wurinsa bai ga komai ba sai ganye, don ba lokacin ‘ya’yan baure ba ne. 14Sai ya ce wa bauren, “Kada kowa ya kara cin ‘‘ya’yanka har abada!” Almajiransa kuwa sun ji maganar.

15Suka iso Urushalima, da shigar su, ya kori masu saye da sayarwa, ya watsar da taburan ‘yan canjin kudi, da kujerun masu sayar da tantabaru. 16Ya hana kowa ya dauki wani abu da za a i ya sayarwa a cikin haikalin.

17Sai ya koyar da su cewa, “Ashe ba rubuce yake ba, “Za a kira gidana gidan addu’a na dukan al’ummai? Amma ku kun mayar da shi kogon yan fashi”. 18Da mayan Faristoci da marubutan attaura suka ji maganar da ya yi, sai suka nami hanyar da za su kashe shi. Amma suka ji tsoronsa domin dukkan taron na mamakin koyarwarsa. 19Kowace yamma kuma, sukan fita gari.

20Da safe suna wucewa, sai suka ga bauren nan ya bushe. 21Bitrus kuwa ya tuna ya ce “Malam, dubi! Baurenan da ka la’anta ya bushe.”

22Yesu ya amsa masu ya ce, “ku gaskata da Allah.” 23Hakika, ina gaya maku, duk wanda ya ce wa dutsen nan tashi ka fada cikin tekun’, bai kuwa yi shakka a zuciyarsa ba, amma ya gaskata haka kuwa zai faru, haka kuwa Allah zai yi.

24Saboda haka ina dai gaya maku, komai kuka yi addu’a kuka roka, ku gaskata cewa samamme ne, zai kuma zama naku. 25Duk sa’add da kuke addu’a ku gafarta wa wadanda suka yi maku laifi, domin Ubanku shima zai gafarta maku naku laifi.” 26(Amma in baku gafartawa mutane laifofinsu ba, Ubanku ma da ke sama ba zai gafarta maku ba.)

27Da suka sake dawowa Urushalima. Yasu na tafiya cikin haikali, sai manyan firistoci, da marubuta, da dattawa suka zo wurinsa, 28suka ce masa, “Da wanne iko kake yin wadanan abubuwa? Ko kuwa wa ya ba ka ikon yinsu? “

29Sai Yesu ya ce masu, “Zan yi maku wata tambaya. ku ba ni amsa, ni kuwa zan gaya maku ko da wanne iko ne nake yin wadannan abubuwan. 30Baftismar da Yahaya yayi, daga sama take ko kuwa daga mutum take? ku bani amsa”.

31Sai suka yi mahuwara da juna, suka ce, “in kuwa muka ce, ‘daga sama take,’ za ya ce, “To, don me ba ku gaskata shi ba? 32In kuwa muka ce, “amma in muka ce ta mutum ce zasu jejjefemu domi suna jin tsoron jama’a, don duk kowa ya tabbata, cewa Yahaya annabi ne. Sai suka amsa wa Yesu suka ce, “Ba mu sani ba” Yesu ya ce masu, “Haka ni kuma ba zan fada muku ko da wanne iko nake yin abubuwan nan ba.”

33

Copyright information for HauULB